Kotu ta daure yan damfara ta Intanet 41 a Anambra

0
122

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a garin Onitsha a jihar Anambra, karkashin jagorancin mai shari’a S. M Shuaibu da Hauwa Inuwa ta yankewa wasu ƴan damfara ta intanet 41 hukuncin ɗaurin shekara daya a gidan yari.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin sada zumunta na X na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa, EFCC.

An ɗaure waɗanda aka yanke wa hukuncin ne bayan sun amsa laifukansu da suka haɗa da samu ta hanyar karya da mallakar takardun damfara, da kuma taimakawa wajen aikata wani laifi bayan da hukumar ta EFCC ta gurfanar da su a kotu.

Dukkan wadanda ake tuhumar sun amsa laifinsu ne a lokacin da aka karanta musu tuhume-tuhume daban-daban, kuma bisa la’akari da rokon da suka yi, lauyan Hukumar EFCC, Michael Ikechukwu Ani, ya roki kotu da ta yanke musu hukunci tare da yanke musu hukuncin da ya dace.

Sai dai lauyoyin wadanda ake tuhuma sun roki kotun da ta yi musu sassauci da kuma tausaya musu wajen yanke musu hukunci, inda suka kara da cewa sun nuna nadamar abin da suka aikataAlkalan sun kuma bayar da umarnin a rika shigar da wadanda aka yankewa hukuncin hidimtawa al’umma daurin bisa ga sashe na 462 na dokar shari’a tare da bayar da umarnin a yi gwanjon kayayyakin da aka kwato daga hannunsu da suka hada da wayoyin hannu da kwamfutaci ta hannun tare da tura kuɗaɗen a Asusun bai ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here