Najeriya ta musanta zargin neman cin hanci daga kamfanin Binance

0
136
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Najeriya ta musanta iƙirarin da kamfanin hada-hadar kuɗi ta intanet, Binance ya yi kan cewa wani jami’in gwamnatin ƙasar ya nemi cin hanci daga jami’in kamfanin na kuɗin kirifto dala miliyan 150.

A ranar Talata ne shugaban kamfanin na Binance, Richard Teng ya yi zargin, wanda aka wallafa a jaridar New York Times ta Amurka da ma wasu jaridun duniya a ci gaba da taƙaddamar da ake yi tsakanin kamfanin na kuɗin kirifto da Najeriya.

Sai dai a wata takardar sanarwa da ta samu sa hannun Rabi’u Ibrahim, mai magana da yawun ministan yaɗa labari na Najeriya, ƙasar ta ce zargin na kamfanin Binance wani yunƙuri ne na “ɓata wa Najeriya suna domin ɓoye ayyukan da yake yi na saɓa ƙa’ida”.

Sanarwar ta ce “babu ko ƙwayar zarra ta gaskiya a zargin da kamfanin na Binance ya yi.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa gaskiyar lamarin shi ne ana ci gaba da tuhumar Binance a Najeriya saboda barin da ya yi aka yi amfani da shafinsa wajen “halasta kuɗaɗen haram da taimaka wa ayyukan ta’addanci da kuma ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen ƙetare ba bisa ƙa’ida ba”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here