Benin ta hana Nijar fitar da fetur saboda rikicin kan iyaka

0
155

Jamhuriyyar Benin ta hana fitar da man fetur daga Nijar ta tashar jiragen ruwa, in ji shugaban ƙasar Patrice Talon a ranar Laraba, inda ya buƙaci Nijar ta sake buɗe kan iyakarta don shigar da kayayyakin Benin tare da daidaita hulɗa tsakaninsu kafin a fara jigilar ɗanyen mai. 

Matakin ya kawo cikas ga shirin Nijar na fara fitar da kayayyaki daga rijiyar manta ta Agadem a watan jiya tare da babban kamfanin mai na China National Petroleum Corp (CNPC) na dalar Amurka miliyan 400. 

An yi hasashen za a daidaita harkokin kasuwanci a yankin bayan da ƙungiyar Ƙasashen Yammacin Afirka ta ɗage takunkumin da ta ƙaƙaba wa Nijar a watan Fabrairun da ya gabata, yayin da take ƙoƙarin hana ta ita da maƙwabtanta Mali da Burkina Faso da ke ƙarƙashin mulkin soja ficewa daga ƙungiyar ta siyasa da tattalin arziki. 

Sai dai Nijar ta rufe iyakokinta daga shigar da kayayyaki daga Benin, kuma ba ta faɗa wa Benin dalilin yin hakan a hukumance ba, in ji Talon a cikin wata sanarwa. 

“Idan kuna so ku loda manku … a cikin ruwanmu, to bai kamata ku kalli Benin a matsayin abokiyar gaba ba,” in ji shi.

“Idan gobe hukumomin Nijar suka yanke shawarar yin hadin gwiwa da ƙasar Benin, to za a yi lodin mai a jiragen ruwa.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here