Majalisar Wakilai ta dakatar da wani kudiri da ke neman hana Babban Bankin Najeriya (CBN) cirar harajin kaso 0.5 cikin 100 daga masu tura kudade ta intanet a kasar.Â
Dan majalisa mai wakiltar mazabar Darazo/Ganjuwa daga Jihar Bauchi, Mansur Manu Soro, ne ya gabatar da kudirin a ranar Laraba.
Sai dai shugaban majalisar ya taka wa kudurin birki.
Wannan kuduri na Honarabul Soro ya biyo bayan umarnin da CBN ya ba wa bankuna sauran cibiyoyin hadahadar kudade cewa su fara cire harajin kashi 0.5% ga duk wanda ya tura kudi ta intanet.
Dan majalisar ya koka da cewa, ana ba da shawarar bullo da sabbin haraji ko kara yawan wadanda ake da su, a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fama da matsin tattalin arziki.
A cewarsa, cire tallafin man fetur da faduwar darajar Naira sun jefa ’yan kasar cikin mawuyacin hali na matsin rayuwa, don haka bai kamata a sake kara musu wani sabon abu da kara jefa su cikin karin matsin tattalin arziki ba.Â
AMINIYA