Kotu ta dakatar da ‘yan majalisar dokokin Rivers 25 

0
139

Wata babbar kotu a birnin Fatakwal na jihar Rivers ta hana mambobin majalisar dokokin jihar 25 ayyana kansu a matsayin ‘yan majalisar dokokin.

Yayin da yake zartar da hukuncin ranar Juma’a, Mai shari’a Charles N. Wali ya ce kotun ta ƙwace kujerun ‘yan majalisun 

‘Yan majalisar 25 ciki har da kakakin majalisar jihar, Martin Amaewhule, da hukuncin ya shafa, masu biyayya ne ga tsohon gwamnan jihar Nyesom Wike, wanda a yanzu shi ne ministan birnin tarayya Abuja.

‘Yan majalisun dai sun fice daga jam’iyyar PDP mai mulkin jihar zuwa APC, a lokacin da dangantaka ta yi tsamin tsakanin Nyesom Wike da gwamnan jihar Siminalayi Fubara.

Bayan ficewarsu daga jam’iyyar ne majalisar jihar ta ce da kore su daga muƙamansu na ‘yan majalisar.

Don haka kotun ta ce ta dakatar da ‘yan majalisar daga halartar zaman majalisar dokokin jihar da ke birnin Fatakwal, ko duk wani wuri da majalisar ta zaɓi ta zauna don gudanar da harkokinta.

Jihar Rivers dai ta faɗa rikicin siyasa, tun bayan da aka fara samun takun saƙa tsakanin gwamnan jihar, Siminalayi Fubara da tsohon gwamna Nyesom Wike, kodayake daga baya gwamnatin tarayya ta shiga tsakani inda ta yi musu sulhu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here