Ganduje ya buƙaci gwamnatin tarayya ta binciki Gwamna Abba

0
76
Gwamna Ganduje
Gwamna Ganduje

Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a cikin wata sanarwa ya buƙaci gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike kan gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf bisa zargin hannu cikin zanga-zanga da aka gudanar a jihar.

Tsohon Gwamna Ganduja ya zargi gwamna Abba Kabir Yusuf da furta kalaman tunzura jama’a a gabanin zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar ‘yan kwanakin da suka gabata a duk fadin kasar.

Ita wannan sabuwar taƙaddama dai, ta kunno kai ne a jihar Kano tsakanin tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya da kuma gwamnan Kano na yanzu na jam’iyyar NNPP kwanaki bayan gudanar da zanga-zangar.

Ku Karanta: Gwamnatin Kaduna ta fito da sabbin matakan baiwa makarantur jihar tsaro 

Idan baku manta ba, Gwamnatin Kano a wata sanarwa da ta fitar ta bakin Hadimin Gwamna a bangaren yada labarai, Sanusi Bature, tayi zargin cewar takardun bincike da ke babbar kotun jihar, an rasa su sakamakon wasu yan zanga-zanga sunyi awaon gaba da wasu.

Sai dai, a sanarwar da Tsohon Gwamnan ya bayar, yayi watsi da wannan zargin.

A cikin sanarwar da Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya fitar ranar Alhamis, ya zargi gwamnan Abba Kabir Yusuf da yin kalaman da suka ingiza jama’a ga yin tarzoma da nufin baƙanta gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“Yakamata gwamnatin tarayya ta binciki gwamnatin jihar Kano domin kowa ya san cewa kafin zanga-zangar, gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi kalamai na tunzura jama’a, saɓani matakan da sauran gwamnonin jihohi suka ɗauka,” in ji Mista Edwin Olofu, mai magana da yawun tsohon gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai tun da farko gwamnatin jihar Kano ta zargi tsohon gwamnan da ɗaukar nauyin wasu matasa da suka fasa kotu tare da sace takardun shari’oi.

“Kowa ya ga yadda mutanen Ganduje suka shigo Kano suka raba wa matasa makamai da kuɗaɗe da kayan shaye-shaye waɗanda suka far wa ɓangarori da dama na al’umma, lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dukiyoyi,” in ji Sanusi Bature Dawakin Tofa mai magana da yawun gwamnan Kano.

BBC Hausa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here