Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin binciken yadda ake ciyar da fursunoni

0
19

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tunji Ojo, ya bayar da umarnin a gaggauta bincikar yadda ake ciyar da fursunonin gidan gyaran hali na Afokang dake Calabar.

A cikin wani hoto mai motsi wanda aka wallafa a Kafar sada zumunta ta Facebook, ya nuna yadda ake cin zarafin fursunonin tare da basu abinci mara inganci.

A cikin wata sanarwar da mai taimakawa mininstan a fannin yada labarai Babatunde Alao, ya fitar a yau yace hoton da aka wallafa ya nuna cewa ba’a bawa fursunonin gidan gyaran hali na Afokang kulawar data dace.

Ku Karanta: Tinubu zai kori wasu daga cikin ministocin sa

Bayan haka sanarwar tace an bayar da umarnin gaggauta bincikar Wannan zargi, tare da daukar alkawarin hukunta duk wanda aka samu da hannu a laifin.

Dole ne a kula da tsafta da abincin masu laifin da kuma walwalar su, inji sanarwar mininstan.

Olubunmi Tunji Ojo,  yace ma’aikatar sa ba zata lamunci duk wani abun da yayi kama da sakaci da aiki ba, inda yace za’a bayyanawa al’umma sakamakon binciken da ya bayar da umarnin gudanarwa, tare da bayyana hukuncin da za’a yiwa jami’an da aka samu da sakaci akan aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here