Gwamnatin Zamfara tayi alkawarin chanzawa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa

0
117

Gwamnatin jihar Zamfara ta sha alwashin sauyawa mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa a karamar hukumar Gummi matsuguni.

Gwamnan jihar Dauda Lawal, ne ya dauki alkawarin hakan bayan ya bayar da tallafin kudi naira miliyan 100, da kayan abinci ga wadanda suka fuskanci ambaliyar.

KU KARANTA: EFCC na neman tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Gwamna Dauda, ya bayyana hakan a lokacin da yake duba irin barnar da ambaliyar ruwan saman tayi a karamar hukumar.

Gwamnan na Zamfara yace za’a bawa duk wanda iftila’in ambaliyar ta  shafa fili a wasu yankunan domin su samu damar gina wasu gidajen.

Haka zalika yace tuni masana ilimin kasa sun kammala nazari da bibiyar sanadiyyar ambaliyar da manufar samar da mafita da hana faruwar hakan a nan gaba.

Dauda ya kuma yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasa yan uwan su a iftila’in.

A yan shekarun baya ma an fuskanci ambaliyar ruwa a sannan kasar nan, wanda hakan yake kawo karancin abinci, rushewar gine gine, da kuma asarar rayuka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here