Hukumar hana cin hanci ta kama sakataren ilimi da shugaban firamare a Kano

0
70

Hukumar karbar koke koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano  (PCACC) ta kama sakataren ilimi da shugaban makarantar Firamare, da karin wasu mutane uku a karamar hukumar Kumbotso, bisa zargin karkatar da kayan makaranta.

Kayan da ake zargin mutanen sun karkatar sun hadar da karafa da sauran kayan katako na zaman dalibai.

Ku Karanta: Gwamnatin Kano ta amince da dokar da ta tilasta gwajin jini kafin aure

An kama mutanen a harabar makarantar Firamaren Gaidar Makada, a jiya asabar, lokacin da suke kokarin kwashe kayayyakin domin siyarwa.

Babban mai kawo wa  Gwamnan Kano rahoto akan ayyukan hukumar karbar koke koke da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Malam Sani Umar, ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Solecebase.

A cewar sa, matasan da suke motsa jiki a cikin makarantar ne suka fahimci cewa ana aiwatar da wani abu na ba daidai ba, wanda hakan yasa aka fuskanci cewa kayan makarantar ake kwashewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here