Ministan Abuja yayi ikirarin kawo hargitsi a jihohin da PDP ke mulki

0
95

Ministan birnin tarayya Abuja kuma tsohon Gwamnan jihar Rivers,  Nyesom Wike, yayi ikirarin kawo hargitsi a jihohin da jam’iyyar adawa ta PDP, take mulka.

Wike yace yana jan kunnen gwamnonin PDP, masu shiga al’amuran jam’iyyar a jihar sa ta Rivers, dasu janye hannun su.

Ku Karanta: ‘Yan Najeriya sun tsunduma cikin nadama – PDP

Wike yayi ikirarin ne a ranar asabar lokacin da yake kada kuri’ar sa a babban taron jam’iyyar PDP na jihar Rivers, wanda aka gudanar a Fatakwal.

Ya kara da cewa har yanzu shi cikakken dan jam’iyyar PDP ne kuma bashi da wani shirin ficewa daga cikin ta.

A Wannan lokaci da muka yi nasarar kammala Wannan babban taro jagorancin PDP a Rivers ya dawo hannun mu, a cewar Wike.

Magoya bayan Gwamnan jihar Rivers Fubara, sun kauracewa babban taron.

Gwamna Fubara a baya ya kasance na hannun daman Wike, wanda hakan yasa aka tsayar dashi takara har ya zama Gwamnan Rivers da taimakon Wike.

Sai dai daga baya dangantaka tayi tsami tsakanin Wike da Fubara, musamman akan zargin da ake yi na cewa Fubara baya yin biyayya ga umarnin Wike.

Wasu daga cikin Gwamnonin PDP karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi, na daga cikin wadanda Wike yake yiwa gargadi dasu janye hannun su akan dambarwar al’amuran jam’iyyar PDP a Rivers.

Gwamnonin suka kafa hujja da cewa tamkar cin amana ne dan jam’iyyar PDP ya karbi mukamin ministar a Gwamnatin APC karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here