Tinubu ya sauka birnin Beijing na kasar China

0
76
Bola Ahmed Tinubu
Bola Ahmed Tinubu

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya sauka a birnin Beijing na kasar China.

Shugaban ya sauka a kasar ta China da sanyin safiyar yau lahadi don fara yin wata ziyarar aiki.

Mai magana da yawun shugaban kasa Ajuri Ngelale, ya bayyanawa manema labarai na fadar shugaban kasa cewa, ana sa ran  Tinubu zai yi tarurruka masu yawan gaske ba tare da bata lokaci ba bayan sauka a kasar Sin.

Ku Karanta: Tinubu ya dawo Najeriya bayan shafe mako guda babu labarinsa

Ngelale yace daga cikin takuran da shugaban Kasar zai yi a China akwai wanda zasu kawo wa kasar nan riba a fannin tattalin arziki.

Shugaba Tinubu zai gana da takwaran sa na kasar Sin wato Xi Jinping don saka hannu akan wasu daga cikin yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla, a bangaren tattalin arziki, aikin gona da kuma tsare tsaren cigaban kasa, inji Ngelale.

Bayan haka shugaban Kasar zai bi sahun sauran shugabannin Afrika a wani taron koli na  kasashen Afrika da China wanda za’a gudanar don tattaunawa akan muhimman babututuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here