PDP zata hukunta mininstan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike

0
131

Jam’iyyar PDP ta nemi tsohon Gwamnan jihar Rivers Kuma ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya gurfana a gaban ta don ladabtar dashi akan zargin yi mata zagon kasa.

Mataimakin daraktan yada labaran PDP na kasa Ibrahim Abdullahi, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da ake ganawa dashi a kafar talbijin ta Channels.

Abdullahi, yace sun nemi Wike, ya gurfana a gaban kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar karkashin jagorancin Tom Ikimi, wanda babban kwamitin PDP na kasa ya kafa.

Ku Karanta: Kwankwaso da Peter Obi zasu koma jam’iyyar PDP

 PDP tace a makonni biyun da suka gabata ta samar da wasu kwamiti guda biyu na ladabtarwa dana sasantawa, sai dai shi Wike, zai gurfana a gaban na ladabtarwa.

Abdullahi Ibrahim, ya kafa hujja da cewa kalaman da Wike yayi na cewa zai kawo hargitsi a jihohin da jam’iyyar PDP take mulki abu ne da ba za’a lamunta ba.

 Haka zalika, yace akwai bukatar Wike ya gyara kalaman da yayi.

A cewar sa, Wike ya nuna jin dadin sa akan yadda yake gudanar da ayyukan sa na mininsta karkashin jam’iyyar APC, tare da bayyana kyamar sa ga Gwamnan jihar Rivers Siminalayi Fubara, na PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here