Kungiyar kwadago tace shugaba Tinubu ya yaudare ta

0
69
Tinubu
Tinubu

Shugabancin kungiyar kwadago na kasa yace shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, yaudare su, bayan da aka wayi gari da ganin sabon farashin litar man fetur da karancin sa a fadin Nigeria.

Shugaban kungiyar Joe Ajaero, ne ya sanar da hakan a yau lokacin da yake bayyana takaicin sa akan karin farashin man fetur, inda yace hakan abu ne da zai kara jefa rayuwar al’umma cikin kunci.

Ku Karanta: Akwai rashin tausayi a karin kudin wutar lantarki da gwamnati ta yi – NLC

Ajaero yace lokacin da suka gana da shugaban Kasa Tinubu a kwanakin baya sun tattauna akan dakatar da sake karin kudin man fetur, lokacin da suka zanta akan batun karin albashin ma’aikata.

Ajaero, ya kara da cewa Gwamnatin tarayya ta yi watsi da alkawuran data dauka na amincewa da kin kara kudin mai, sannan yace babu makawa karin farashin man zai kara gurgunta masana’antu da kasuwanci, har ma da jefa mutane cikin kunci.

Kungiyar kwadago ta kara da cewa babu daya daga cikin alkawuran da gwamnatin Tinubu ta cika, ma’ana har yanzu gwamnatin bata fara biyan albashi da tayi alkawarin karawa ba na mafi karanci naira dubu 70.

A safiyar yau Talata ne aka wayi gari da ganin sabon farashin litar man fetur a gidajen man kamfanin mai na NNPCL daga 620, zuwa 855, zuwa 890, a wasu jihohin.

A gidajen man yan kasuwa kuwa farashin litar man takai naira 1200.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here