Kyauta Dillaliya ta bayyana dalilin ta na neman takarar kujerar Kansila

0
133

Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Fatima Nayo Adam, wadda aka fi sani da kyauta dillaliya ta bayyana dalilin ta na yanke shawarar neman takarar kujerar Kansila a zabukan kananun hukumonin jihar Kano dake tafe.

Kyauta Dillaliya wadda tayi fice a shirin tashar Arewa 24, mai nisan zango Dadin Kowa, ta sanar da matsayar data dauka a yau lokacin da take zantawa da jaridar Daily News 24.

Kyauta tana neman takarar Kansilan mazabar Dorayi a karamar hukumar Gwale, karkashin jam’iyyar NNPP.

Tace daga cikin dalilan ta na tsayawa takarar akwai tallafawa matasan da suka gaza yin aure da kuma taimakawa mata marasa aikin yi, inda tace ta fahimci bata da hanyar da zata taimaka har sai ta shiga siyasa.

A cewar ta, ta gane cewa matasa da dama suna da aikin yi amma basu da matsugunin da zasu saka matan su in sun yi aure, haka ne yasa zata yi amfani da damar ta in ta zama Kansila ta samar da filayen da zai ishi mutum zama da iyalan sa ta kuma bayar da su kyauta ga matasan.

Kyauta Dillaliya ta kara da cewa zata taimakawa wasu matasan da gonaki har ma da kayan aikin gona sakamakon cewa akwai arziki mai yawa a fannin noma, tare da taimakon mata da jari.

Dillaliya wadda tace ta jima a harkar siyasa, sannan tace tana son tallafawa almajirai da Kuma yan matan da suka kasa yin aure suna yawo akan tituna domin yin barace barace.

A cewar kyauta Dillaliya abin takaici ne a rinka ganin kananun yaran da shekarun su basu wuce 5 suna yin bara don neman abinda zasu ci, inda tace hakan yana jefa rayuwar yara da yawa cikin hadari, amma tace zata taimaki masu irin wannan kalubalen don samun rayuwa mai inganci.

Daga karshe Kyauta Dillaliya tace tuni ta kammala siyan tikitin nuna sha’awar ta, ta neman zama Kansila a mazabar Dorayi, in da tace bukatar ta, ta neman zama Kansila ba abun a mutu ko ayi rai bane babban abinda take bukata shine addua’r mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here