Za’a zartarwa da fursunoni fiye da dubu 3 hukuncin kisa

0
69

Akalla fursunonin dake gidajen gyaran hali 3,590 ne suke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a fadin kasar nan.

Hukumar kula da gidajen gyaran hali ta kasa ce ta shaida hakan.

Babban jami’in hukumar kula da gidajen gyaran hali na kasa Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a birnin tarayya Abuja.

Ku Karanta: Hukumar hana cin hanci ta kama sakataren ilimi da shugaban firamare a Kano

A cewar sa akwai fursunonin da yawan su yakai dubu 84,74, maza 82,821 sai mata 1,920, a daukacin gidajen gyaran halin dake fadin kasar nan.

Yace Wannan alkaluma an samar da su a ranar 3 ga watan da muke ciki wato jiya Talata.

Hukumar kula da gidajen gyaran halin tace a cikin fursunonin akwai mutane 57,750 da suke jiran shari’a maza da mata.

Su kuwa wadanda suke jiran a zartar musu da hukuncin kisa sun hadar da maza 3,517 da Kuma mata 73.

A cewar Umar Abubakar, babban kalubalen da suke fuskanta shine mafi yawancin fursunonin jiran shari’a suke yi ba tare da an yanke musu hukunci ba.

Sai dai yace hukumar kula da gidajen gyaran halin tayi hadin gwuiwa da jami’ar daukar karatu daga gida wato NOUN, inda fursunoni da dama suka shiga makarantar, sannan ya ce akwai fursunonin da tuni sun kammala digiri a gidajen yarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here