Gwamnatin Kano ta dauki matakin shari’a akan wasu makarantu masu zaman kansu

0
90

Gwamnatin jihar Kano karkashin hukumar kula da makarantu masu zaman kansu zata gurfanar da makarantun Crescent International da Ibni Mas’ud dake kabuga sai kuma Matasa Secondary School dake zaune a unguwar Na’ibawa.

A cikin wata takardar shigar da kara da aka gabatar a gaban kotun majistare Mai Lamba 36 da dake Gyadi-Gyadi an zargi makarantar Crecent International da kin biyan kudaden haraji kamar yadda doka ta tanada na biyan kaso goma cikin dari cikin kudin shigar da makarantar ta tattara kuma hakan ya sabawa sashi na 11 na dokar hukumar kula da makarantun.

Ku Karanta: Hukumar hana cin hanci ta kama sakataren ilimi da shugaban firamare a Kano

An shigar da karar a ranar litinin data gabata, sannan kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 9 ga watan da muke ciki na Satumba.

Su kuwa makarantun IBN-Masudu da Matasa sakandire kotun ta bayar da umarnin rufe su baki daya sakamakon samun su da laifin karya dokar hukumar kula da makarantun masu zaman kansu da makarantun sa kai.

Tun a baya hukumar ta zargi makarantun IBN-Masudu da Matasa secondary dake da laifin zuba dalibai a cikin gine gine marasa ingancin da zasu iya cutar da lafiyar daliban, hukumar tayi zargin a lokacin da takai ziyarar aiki makarantun.

Sakataren gudanarwa na hukumar Baba Abubakar Umar, yayi alkawarin cewa ko kadan ba zasu daga kafa ba, akan hukunta duk makarantar da aka samu da karya doka.

Sakataren hukumar yace gwamnatin Kano ta bashi cikakken goyon bayan tsaftace makarantun da suke karkashin kulawar hukumar sa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here