Daliban da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun su a kasashen waje sun shiga kuncin rayuwa

0
56
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Fitaccen lauyan nan dan Nigeria mazaunin kasar Burtaniya Dr Bulama Bukarti, yace daliban da gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun su zuwa kasashen ketare sun shiga matsalar rashin kudaden gudanar da rayuwa saboda rashin isashshen kudin alawus da ake basu.

Jaridar Daily News 24 ta rawaito cewa Dr Bukarti, ya bayyana hakan a lokacin da ake zantawa dashi a wani shiri mai suna fashin baki a ranar litinin data gabata.

Bukarti wanda suka gabatar da shirin tare da Babba Hikima, wanda shima lauya ne, ya sanar da cewa wasu daga cikin daliban sun aikowa gwamnatin Kano wasika akan irin kalubalen da suke fuskanta.

Ku Karanta: Matsin rayuwa: Magidanci ya rataye kansa har lahira a Jigawa

Yace kafin yanzu gwamnatin Kano tayi alkawarin bawa kowanne dalibi dala 150 a kowanne wata sai dai hakan ya canja inda a yanzu yace dala 62.50 ake basu.

Bukarti ya kara da cewa kudin da ake bawa daliban bai wuce naira dubu 100 a kudin Nigeria ba, inda yace tabbas sunyi kadan mutum ya iya gudanar da rayuwar sa ta tsawon wata daya da naira dubu 100 a kasashen waje da suka fi Kasar nan tsadar rayuwa.

Sannan ya kafa hujja da cewa wasu daga cikin daliban sun bar iyalan su a nan Nigeria kuma a cikin kudin da ake basu suke aikowa da iyalan nasu wani kaso na cikin kudin a kowanne lokaci.

Dr Bukarti ya kara da cewa hakan yasa dole wasu daga cikin daliban sun koma yin gararamba a kasashen da suka je yin karatu.

Dr Bukarti, yace lokacin daya ziyarci wasu daliban da gwamnatin Kano ta tura yin karatu a Uganda su kusan 36, tuni 12 daga cikin su sun koma gida Kano saboda rashin isashshen kudin da zasu yi rayuwa, haka ne yasa Bukarti ya roki gwamnatin Kano akan ta dauki matakin shawo kan Wannan matsala.

Akan hakan jaridar Daily News 24 tayi kokarin jin ta bakin kwamishinan ilimi mai zurfi na Kano Dr Yusuf Ibrahim Kofar-Mata, sai dai bai samu damar daga Kiran waya da muka yi masa ba, haka zalika bai samu damar bamu amsa akan rubutaccen sakon da muka aike masa ba.

Idan za’a iya tunawa a watan Octoba na shekarar 2023, gwamnatin Kano ta dauki nauyin karatun yan asalin jihar su 1001, zuwa karatu a kasashen Uganda da India, don yin karatun digiri na biyu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here