Ƴan Najeriya na jiran sakamakon binciken da aka gudanar kan Seaman Abbas

0
68
Seaman Abbas
Seaman Abbas

Yan Najeriya suna ta zazzafar mahawara shafukan sada zumunta game da zargin cin zarafi da kuma azabtar da wani sojan ruwa bayan da matarsa ta bayyana cewa an ɗaure shi tsawon shekara shida cikin mummunar yanayi har ya samu taɓin hankali.

Matar sojan ruwan mai suna Abbas Haruna mai suna Hussaina ta bayyana cikin wani faifen bidiyo da tayi hira da gidan rediyon Berekete a Abuja cewa an gana masa uƙubar da ta wuce misali.

Ku Karanta: Babu tattaunawa tsakaninmu da wata kasa kan kafa sansanin soja – Gwamnatin Najeriya

Matar ta bayyana wasu zarge-zargen cewa ba a yi wa mijinta da ma su iyalansa ɗin adalci ba.

Hussaina, ta bayyana cewa mijin nata ya samu saɓani ne da wani babban hafsan soja, inda tun a lokacin aka kama shi, aka tsare, kuma a cewarta kusan shekara shida ke nan yana tsare.

Bidiyon na Hussaina ya karaɗe shafukan sada zumunta, inda aka riƙa yaɗa shi, wasu na zagi, wasu na Allah wadai, wasu kuma suna cewa a dai yi bincike.

Babban abin da ya ja hankalin mutane shi ne yadda Hussaina ta bayyana yadda ta sha faɗi-tashi da tafiye-tafiye tsakanin Kaduna da Taraba da Abuja da Gombe duk a kan mijin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here