Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin Kano

0
57

Wata babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin hana wasu jam’iyyun siyasa 19 kawo cikas ga hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC wajen shirya zaben kananun hukumoni dake tafe a wata mai kamawa.

Mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji, ne ya bayar da umarnin a jiya bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Kano KANSIEC ta shigar da jam’iyyun kara akan zargin kawo mata tarnaki wajen shiryawa da kuma gudanar da zaben kananun hukumonin.

karanta karin wasu labaran: NNPP ta sanar da mutanen da zasu yi mata takara a zabukan kananun hukumonin Kano

Jam’iyyun siyasar da aka shigar da karar sun hadar da NNPP, PDP, APC da sauran wasu jam’iyyun.

A lokacin da yake yanke hukuncin mai shari’a Ma’aji, ya haramtawa jam’iyyun aikata duk wani abun da zai kawowa hukumar KANSIEC matsala wajen gudanar da zaben, har sai an sake sauraron karar.

Haka zalika an haramtawa jam’iyyun da wakilan su yiwa KANSIEC zagon kasa wanda zai bawa hukumar zaben matsala a aikin ta na shirya zaben.

Kotun ta jingine sauraron karar har zuwa ranar 10 ga watan October, wanda a cikin aa ne za’a gabatar da zaben kananun hukumonin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here