Majalisar wakilai taki amincewa da kudirin neman gwamnatin tarayya ta tallafawa mutanen da ambaliyar ruwan sama ta shafa a birnin Maiduguri na jihar Borno.
Wasu daga cikin yan majalisar sun gabatar da kudirin neman Gwamnatin tarayyar ta tallafawa Maiduguri da naira miliyan dubu 300, ga mutanen da suka fuskanci ambaliyar da kayayyakin jin kai.
Karanta karin wasu labaran:Sojoji sun kashe ‘yan bindiga da dama a Neja da Borno
Idan za’a iya tunawa a kwanakin da suka gabata ne tafkin Alou ya yi ambaliyar ruwan data mamaye daukacin birnin Maiduguri, kuma tayi sanadin mutuwar fiye da mutane 40, da jikkatar mutane da dama bayan rusau a wuraren gwamnati, gidajen mutane da sauran su.
A zaman majalisar na yau laraba dan majalisar wakilai Amos Magaji, dake wakiltar mazabar Jaba da Zangon Kataf ne ya shigar da kudirin bukatar gaggawa akan neman taimakawa wadanda suka fuskanci ambaliyar ruwan.
Yace ambaliyar ta lalata kasuwanni, asibitoci, makarantu, da sauaran gurare masu muhimmanci da yace a yanzu ba zasu yi amfani ba in har ba’a gyara su ba.
Bayan Wannan Amos Magaji, yace ambaliyar ta lalata babbar Cibiyar kula da masu fama da cutar daji wato Cancer Kuma itace babbar Cibiyar kula da masu fama da cutar daji mafi girma a fadin kasar nan.
Bisa hujjar daya bayyana yace in har ba’a dauki matakin gaggawa ba nan gaba kadan al’ummar Borno ka’iya kamuwa da cutuka masu yaduwa.
Shima Inuwa Garba, dake wakiltar Yamaltu Deba, daga jihar Gombe, ya roki gwamnatin tarayya ta bawa Borno tallafin naira biliyan dari 3, don taimakawa wadanda suka fuskanci ambaliyar.
Sai dai wasu daga cikin yan majalisar sun kalubalanci rokon bayar da tallafin a lokacin da kakakin majalisar Tajuddeen Abbas, ya bayar da dama ga yan majalisar su bayyana ra’ayoyin su na goyon bayan bayar da tallafin ko akasin haka.
Yan majalisar sun ce tun tuni wasu daga cikin hukumonin gwamnatin sun bawa Borno tallafin kudaden da yawan su yakai biliyoyi.
Daga karshe majalisar ta roki gwamnatin tarayya ta gyara asibitin koyarwa na Maiduguri, da gyara fadar Shehun Borno, sai gyaran gidan gyaran hali na Maiduguri wanda shima ambaliyar ta lalata.