An fara samun sabon layin ababen hawa a gidajen man fetur na birnin tarayya Abuja, wanda hakan yasa masu ababen hawa shafe awanni masu yawa kafin su samu damar shan man.
Hakan ya samo asali bayan masu gidajen mai na yan kasuwa sun rufe nasu gidajen man tare da kin siyar da shi ga mutane.
Karanta karin wasu labaran: Man fetir din Najeriya ya fara kwantai a kasuwar duniya
Wani binciken da jaridar Daily Trust, ta gudanar a ranar talata ya nuna cewa mafi yawancin gidajen man dake birnin tarayya Abuja sun kasance a rufe, sannan akwai dogwayen layukan ababen hawa a gidajen man da suka bude musamman gidajen man NNPCL da sauran su.
Gidan man NNPC dake kan hanyar Zuba zuwa Kubwa ya kasance a bude, sai dai akwai layin ababen hawa fiye da misali, Kuma hakan ya zama sanadin shigar mutane da dama cikin kunci da rashin samun damar zuwa wajen da suke so saboda karancin ababen hawa a kan tituna.
Sannan an samu tashin farashin man sosai a wajen masu Sana’ar bunbututu.
Duk da haka akwai majiyar da ta nuna cewa manyan dillalan man fetur sun fitar da litar man fetur fiye da miliyan 50 daga matatar Dangote a makon daya gabata.
Wannan matsala ana kyautata zaton ta samo asali bayan da hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa PENGASSAN, tace dillalan man fetur masu zaman kansu basu da damar siyo man fetur kai tsaye daga matatar Dangote, sai dai su rika siya daga hannun hukumonin Gwamnatin tarayya.
Masana harkokin tattalin arziki sun tabbatar da cewa in har aka kyale yan kasuwa suna siyan man fetur kai tsaye daga hannun Dangote hakan zai iya saukaka farashin sa a kasar nan.