Shugaba Tinubu zai sauke wasu daga cikin ministocin sa

0
43
Tinubu

Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa shugaban kasa Tinubu zai yiwa majalisar zartarwa taza da tsifa wajen yiwa ministocin sa garambawul nan bada jimawa ba.

Fadar shugaban kasar tace za’a yiwa ministocin garambawul ne bayan duba yanayin aikin kowanne minista ta hanyar duba kokarin kowanne daga cikin su bayan shugaban kasar ya karbi rahoto akan aikin da suka gudanar a watannin da suka wuce.

karanta karin wasu labaran: Kungiyar kwadago tace shugaba Tinubu ya yaudare ta

Jaridar Punch ta rawaito cewa shugaban kasar da bakin sa ya tabbatar da cewa za’a yiwa majalisar gyara nan da kwanaki masu zuwa.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai da tsare tsare Bayo Onanuga, da mai taimakawa shugaban kasar a fannin sabbin kafafen sadarwa O’Tega Ogra, ne suka sanar da hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa a yau laraba.

O’Tega Ogra, yace mai taimakawa shugaban kasa a fannin tsare tsaren harkokin gwamnati Hadiza Bala Usman, ce ta mikawa shugaba Tinubu rahoton kokarin kowanne minista, wanda yace an bi duk ka’idojin da suka dace wajen tantance kokarin da ministocin suka yi daga lokacin da aka basu mukamin zuwa yanzu.

Shugaba Tinubu yace za’a cire duk wanda ya gaza yin kokari a ma’aikatar da aka bashi, sannan wadanda suka yi aiki tukuru zasu cigaba da kasance a kan mukamin minista.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here