Alumma’r gari sun kashe shugabannin yan fashin daji 2

0
87

Rahotanni sun tabbatar da kisan wasu manyan yan fashin daji 2 da suka kware wajen kisan mutane da yin garkuwa da su a jihar Zamfara.

Yan fashin dajin da suka gamu da ajalin su sun hadar da Sani Black da Kachalla Makore.

Mutanen biyu sune wadanda suka addabi kauyen Dansadau da kewayen sa da ayyukan ta’addanci har ma da wasu sassan karamar hukumar Maru.

Karanta karin wasu labaran:Mun yi fata-fata da sansanonin ‘yan ta’adda guda 3 a Zamfara – Sojoji

Da yake tabbatar da kisan yan fashin dajin mai bawa gwamnan jihar Zamfara shawara a fannin kafafen sadarwa da yada labarai, Alhaji Mustafha Jafaru, yace an kashe Sani Black, a ranar lahadi a kauyen Yar-Tasha, Sai Kachalla Makore da aka hallaka a Kauyen Kunkeli ranar Talata duk a karamar hukumar Maru.

A cewar sa an kashe manyan yan fashin dajin tare da masu taimaka musu 23.

Al’ummar dake aikin samarwa kansu da kansu tsaro a Zamfara ne suka kashe su, tare da jami’an tsaro.

Bayan kisan kwantan bauna da aka yiwa Black a ranar lahadi, Kachalla Makore, ya debi mabiyan sa zuwa karbo gawar dan uwansa wanda shima hakan ya zama sanadin mutuwar sa bayan yaje daukar fansa.

An kashe black tare da mayakan sa 8, sai Makore da aka kashe tare da mayakan sa 15.

Kafin mutuwar Makore sai da ya lalata wata motar sojoji sannan ya jikkata sojoji biyu a kauyen Kunkeli.

Mai taimakawa gwamnan na Zamfara ya roki al’umma su cigaba da taimakon jami’an tsaro da bayanan sirri akan duk labarin yan ta’addan da suka samu.

A kwanakin baya dai gwamnatin tarayya ta umarci karamin ministan tsaro Bello Matawalle, da sauran jami’an tsaro su koma jihar Zamfara da zama ko za’a samu nasarar kakkabe ta’addanci a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here