Gwamnatin Kano ta ciyo bashin naira biliyan 177

0
41
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano ta ciyo bashin naira biliyan 177 da miliyan dari 4, daga hukumar samar da cigaba ta kasar Faransa da manufar yin sabbin gyare-gyare a matatar ruwan sha dake garin Tamburawa.

Gwamnatin tace hakan zai fadada kokarin ta na samar da ruwan sha ga al’ummar jihar.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin Kano

A cewar gwamnatin aikin da zata yi zai taimaka wajen samar wa mutanen jihar Kano ruwan shan da suke bukata, bisa hujjar cewa al’ummar jihar suna karuwa a cikin saurin kuma kowa yana da bukatar ruwan da zai sha.

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya bayyana hakan a wani taron karawa juna sani da aka shirya na wuni biyu, wanda kwamishinan ruwa na Kano Alhaji Ali Haruna Makoda, ya wakiltar.

Taron ya samu halartar wakilai daga jihohin Plateau, Enugu, da Ondo.

Kwamishinan yace za’a yi aikin karkashin shirin gwamnatin tarayya na farfado da yanayin samar da ruwan sha a birane, Kuma ma’aikatar albarkatun ruwa ta kasa ta amince da yin aikin samar da ruwan shan.

Alhaji Ali Haruna Makoda, yace tun a baya yanayin annobar cutar Coronavirus ne ya hana kammala aiki na Tamburawa, da Kuma sauran wasu dalilai, sai dai yace nan da shekara biyu zasu kammala aikin.

A nasa jawabin shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano Garba Ahmad Bichi, yace aikin ya hadar da gina sabuwar madatsar ruwa da zata rika samar da tataccen ruwan sha lita dubu 250 a kowacce rana.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here