Kotu tayi watsi da bukatar APC akan zaben kananun hukumomin Kano

0
55

Wata kotun tarayya dake zaune a jihar Kano tayi watsi da bukatar jam’iyyar APC ta neman a dakatar da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar KANSIEC daga gudanar da zabukan kananun hukumoni da za’a yi a wata mai kamawa.

Jam’iyyar APC ce ta shigar da karar a ranar 20 watan Satumba.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin Kano

Wadanda aka shigar karar sun hadar da majalisar dokokin jihar Kano, kwamishinan shari’a na jihar, da Kuma karin wasu mutane 11, inda APC take bukatar kotu ta haramtawa hukumar zabe ta Kano gudanar da zaben kananun hukumomi 44 na jihar.

Mai shari’a Simon Amobeda, ne ya yanke hukuncin a ranar laraba.

Karin bukatun da APC ta nemi kotun ta amince sun hada da neman hana kowacce jam’iyyar siyasa shirin shiga zabukan.

Mai shari’a Ambode, ya ce jam’iyyar APC bata da damar dakatar da KANSIEC daga shirin ta na gudanar da zaben a ranar 26 ga watan Octoba.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga watan Octoba wanda ya rage kwanaki 22 a gudanar da zaben, tare da jan kunnen daukacin jam’iyyun siyasa akan kiyaye aikata duk wani abun da zai kawo cikas ga umarnin Kotu.

Shima mai shari’a Ado Ma’aji, na wata babbar kotun jihar Kano ya bayar da umarnin hana duk wasu jam’iyyun siyasa kawo wa KANSIEC tangarda akan shirya zaben kananun hukumomin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here