Gwamnatin tarayyar kasar nan ta samu tallafin dala dubu 600 da za’a yi amfani da su wajen taimakawa mutanen da suka fuskanci ambaliyar ruwa da Kuma inganta harkokin kiwon lafiya.
Gidauniyar Bill da Melinda Gates, ce ta bayar da tallafin.
Karanta karin wasu labaran:Tafkin Lagdo zai haifar wa jihohin Nigeria 11 ambaliyar ruwa
Kai tsaye gidauniyar ta bayar da tallafin ne saboda a magance matsalar ambaliyar ruwan da aka samu a jihar Borno, sai kuma karin dala miliyan 5 da za’a yi amfani da su a makarantar koyar da sana’o’i dake Legas da kuma inganta harkokin noma da tattalin arziki.
An bayar da tallafin ne Lokacin da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya gana da gidauniyar Bill da Melinda Gates, a wani bangare na babban taron majalisar dinkin duniya karo na 79 wanda aka yi a birnin New York dake kasar Amurka.
Shettima, ya kara tabbatar da kokarin da yace shugaban kasa Tinubu yake yi na don samar da kyakyawan yanayi a fannin samar da abinci mai gina jiki, inganta lafiya, habbaka noma, da sauran su.
A wata sanarwar da mai taimakawa mataimakin shugaban kasar a fannin kafafen sadarwa da yada labarai Stanley Nkwocha, ya fitar Shettima yace gwamnatin su ta himmatu matuka wajen magance kalubalen rashin abinci mai gina jiki ga al’ummar Najeriya.
A cewar sa gwamnatin tarayya zata yi amfani da kyakyawan tsarin shugabanci don kawar da matsalar.
Bayan haka gwamnatin tarayya tace zata bayar da izinin shigo da irin shuka wanda aka tabbatar suna da kyau daga kasashen waje, sai Kuma daga darajar shirin samar da rogo wanda shima yake taka muhimmiyar rawa a tattalin arziki.