Cutar amai da gudawa ta kashe mutane 9 a Jihar Yobe

0
62

Cutar amai da gudawa data barke a jihar Yobe tayi sanadin mutuwar mutane 9 a kananun hukumomin jihar 5.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Lawan Gana, yace an samu bullar cutar a kananun hukumomin Gujba, Fune, Machina, Nangere da Nguru.

A cewar sa adadin mutane 132, aka tabbatar sun kamu da cutar zuwa ranar 25 ga watan Satumba, amma tuni an sallami marasa lafiyar su 112 daga asibiti.

Karanta karin wasu labaran:Diphtheria: Akalla yara 30 sun mutu a Yobe

Yace ambaliyar ruwan saman da ake samu ce ta haddasa cutar ta Cholera.

Tun kafin samun barkewar cutar anja hankalin al’ummar jihar Borno da kewaye akan yiwuwar barkewar cutuka masu yaduwa, sakamakon yadda ambaliyar ruwa ta mamaye jihar ta Borno.

Jihar Yobe ta kasance babbar makwabciyar jihar Borno kuma hakan zai iya haifar da barkewar cutar a Yobe da sauran jihohin arewa maso gabas.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here