Akalla mutane 29 ne suka mutu sannan gidaje dubu dari 321, da gonaki 858,000, suka salwanta a jihar Kebbi, saboda ambaliyar ruwa.
Kwamishinan yada labarai na jihar Yakubu Ahmad, ne ya sanar da manema labarai cewa in ba’a kaiwa al’ummar da al’amarin ya shafa ba za’a iya fuskantar karancin abinci a jihar da Nigeria baki daya.
Karanta karin wasu labaran:Najeriya ta samu tallafin dala dubu 600 saboda ambaliyar ruwa
Yace a yankunan da aka samu ambaliyar akwai gonakin shinkafa, masara da sauran kayan abinci wanda tuni sun lalace.
Kwamishinan yace tun kafin hukumar kula da yanayi ta kasa tayi hasashen samun ambaliyar a Kebbi, tuni lamarin ya ta’azara a kananun hukumoni 16, Sakamakon ruwan da aka saki daga tafkin Goronyo.
Sannan gwamnatin tace duk da ta dauki mataki akan lamarin har yanzu akwai kalubale mai yawa dangane da matsalar ambaliyar.