Gwamnatin tarayya zata hana dogaro da kayan abincin kasashen ketare

0
58
Gona - Neja
Gona - Neja

Gwamnatin tarayyar Nigeria tace ta shiryawa daukar matakan hana kasar dogaro da kayan abinci da ake shigowa dasu daga kasashen waje.

Ministan kudi Wale Edun, yace gwamnatin tana da manyan tsare tsaren habbaka noma da inganta samar da abincin da kasar ke bukata.

Edun, ya bayyana hakan a ranar alhamis lokacin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani da Kuma murnar bukukuwan cikar Nigeria shekaru 64 da samun yancin kai Wanda za’a yi bikin a wata mai kamawa.

Yace dole ne a kawo karshen dogaron da Nigeria tayi akan samun abinci daga wasu kasashen.

Yace gwamnatin tarayya ta himmatu matuka wajen taimakawa kananun manoma da kayan noma kamar su taki da irin shuka, a karkashin shirin gwamnatin tarayya na habbaka noma da aikin gona.

Tallafin zai hada da masu noman damuna da kuma masu noman rani don samar da abincin da ake bukata.

Ministan kudin yace wasu daga cikin matakan da gwamnatin ta dauka na dakile hauhawar farashin kayan masarufi a baya bayan nan sun hadar da shigo da masara da alkama don daidaita farashin kayan abinci a kasuwanni.

Sannan yace rage shigo da kayan abinci shine babbar hanyar da zata kawo wa Nigeria mafita daga koma bayan tattalin arziki da ake ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here