An fara tantance wadanda za’a bawa tallafin ambaliyar Maiduguri

0
63

An fara tantance mutanen da za’a bawa tallafin ambaliyar ruwan da aka fuskanta a Maidugurin jihar Borno.

Mutanen da za’a bawa tallafin sun kai 7000, kuma an fara tantancewar a mazabar Limanti dake kwaryar birnin Maiduguri.

Ana aikin tantancewar a Makarantar Firamaren ibn Garbai Elkanemi.

Karanta karin wasu labaran:Jonathan ya bayyana dalilin sa na cire Sarkin Kano daga shugabancin CBN

Wannan shine karo na biyu da fara tantancewar bayan wadda aka yi a Gwange, Kuma gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, ne ya kaddamar da aikin bayar da tallafin.

An bayyana sunayen mutanen da ambaliyar ruwan ta shafa a gidan hakimin yankin don tantance su.

Sannan an samar da wajen kai duk wani korafin da mutanen zasu iya kaiwa.

Shugaban kwamitin bayar da tallafin Engr. Baba Bukar Gujibawu, yace zasu tabbatar da adalci ga wadanda za’a bawa tallafin.

Baba Bukar, ya roki mutanen su kwantar da hankalin su, yana mai cewa babu wanda ba zai samu tallafin ba, in har yana daga cikin wadanda suka fuskanci ambaliyar.

A ranar talata data gabata gwamnan jihar ta Borno Babagana Umara Zulum, ya kaddamar da rabon kayan tallafin ga mutane fiye da 5000, a mazabar Gwange 1.

Idan za’a iya tunawa a cikin Wannan wata ne jihar Borno ta fuskanci mummunar ambaliyar ruwa data hallaka mutane fiye da 40, rushe gidaje da Kuma lalata gonaki, sakamakon fashewar tafkin Alou.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here