EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku

0
10

Tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, ya kwana a hannun jami’an hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa don amsa wasu tambayoyin hukumar.

EFCC ta kama Ishaku, saboda zargin da ake yi masa na almundahanar kudaden kananun hukumonin jihar da yawan su yakai naira miliyan dubu 27.

EFCC ta kama shi ne jiya alhamis a gidan sa dake birnin tarayya Abuja.

Karanta karin wasu labaran:Yahaya Bello ya shigar da EFCC kara gaban kotun Koli

Wata majiya ta tabbatar wa da jaridar Punch, cewa ana tuhumar Darius, da aikata lefuka15.

Cikin wata takarda mai dauke da kwanan watan 27 ga watan Satumba, wadda ta fito daga hukumar EFCC an bayyana Ishaku da babban sakataren hukumar kula da kananun hukumoni na jihar Taraba, a matsayin wadanda ake zargi sun hada baki tare da karkatar da kudaden da karin wani mutum daya.

A cikin karar da EFCC ta shigar da Ishaku, gaban wata Kotun tarayya an zargi mutanen da kwashe wasu adadin kudaden kananun hukumonin Taraba a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2016, Kuma sun yi amfanin kansu da kudaden.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here