An kori dan takarar gwamnan jihar Benue daga gidan sa saboda cin bashi

0
69

An kori É—an siyasar jihar Benue daga gidansa bayan da matarsa ta jinginar da gidan ta ciyo bashi.

Mutumin da aka kora daga gidan nasa shine tsohon dan takarar Gwamnan jihar Benue na jam’iyyar ACC, Ewaoche Benjamin Obe.

Jaridar DAILY POST ta ce gidan yana unguwar Sagwari Layout a karamar hukumar Bwari ta birnin tarayya Abuja.

Karanta karin wasu labaran:Shari’ar da ake min bita da kullin siyasa ne – Donald Trump

Matar dan siyasar mai suna Christiana Obe ta auri Obe a shekarar 2006.

Ma’auratan sun kasance yan asalin karamar hukumar Ogbadibo ta jihar Benue.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru a ranar Laraba 25 ga watan Satumba na 2024.

Obe, wanda ke kan hanyar sa ta zuwa Benue, shine ya tabbatar da cewa wasu jami’an tsaro sun fitar da shi daga gidan sa, bayan ya samu labari daga kiran wayar da akayi masa don sanar da shi halin da ake ciki.

Jin haka ne yasa dan siyasar juya motar sa zuwa gidan nasa.

Amman zuwan sa ke da wuya aka nuna masa takardun kotu dake nuni da cewa an karbe gidan nasa sakamon bashin da ake bin matar sa bayan ta jinginar da kafin karbar bashin.

Ko da aka nemi jin ta bakin matar tace babu bukatar tace komai akan lamarin daya faru da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here