Shirin sabuwar zanga zangar 1 ga watan Oktoba ya dauki sabon salo

0
52

Masu shirya wata sabuwar zanga zangar a ranar 1 ga watan Oktoba, mai kamawa sun ce jami’an yan sanda da na farin kaya basu isa su hana su yin abin da suka yi niyya ba.

Mutanen sun rubutawa shugaban yan sanda na kasa Kayode Egbetokun, wasikar neman ya basu jami’an tsaro da zasu kare lafiyar su yayin zanga zangar, sannan suka ce yin zanga zanga yancin kowanne dan kasa ne don haka babu mai ikon hana su fitowa kan tituna.

A ranar talata kasar nan zata yi bikin cika shekaru 64 da samun yancin kai, Kuma a Wannan rana ce wasu matasa ke shirin gabatar da zanga zangar tsadar rayuwa bayan cire tallafin man fetur, da karya darajar naira da gwamnatin tarayya ke cigaba da yi.

Karanta karin wasu labaran:Najeriya ta samu tallafin dala dubu 600 saboda ambaliyar ruwa

Juwon Sanyaolu, da Damilare Adenola, sune mashirya fita zanga zangar, har ma suka ce tuni suka fara tattarawa da wayar da kan al’umma akan zanga zangar a sannan Nigeria baki daya

A cewar shugabannin zanga zangar sun rubutawa jami’an tsaro wasika akan wajen da za’a yi taron, sannan suka ce kundin tsarin mulkin kasa ya basu damar yin hakan.

Sun ce a birnin tarayya Abuja zasu taru a dandanlin Eagle Square, Kuma a nan ne za’a yi taron murnar cikar Nigeria shekaru 64 da samun yancin kai, sai Legas da za’a yi taron a karkashin gadar Ikeja.

Daga cikin sharudan su na janye zanga zangar akwai dawo da tallafin man fetur da suka ce shi kadai ne zai hana fita zanga zangar.

Sai dai tuni shugaban yan sandan kasa ya bawa jami’an sa umarnin yin shirin ko ta kwana dangane da zanga zangar, tare da neman kwamishinonin yan sanda, su wayar da kan kungiyoyin fararen hula da daidaikun mutane akan kaucewa shiga zanga zangar.

Yayin da shi kuma shugaban zanga zangar Omoyele Sowore, ke cewa matasan da suke shirin fita zanga zangar basa tsoron barazanar jami’an yan sanda kuma za su fito zanga zangar kamar yadda aka shirya.

Idan za’a iya tunawa a farkon watan Ogustan shekarar da muke ciki ne aka gudanar da zanga zangar samar da shugabanci na gari, wadda ta rikide zuwa tarzoma da kashe al’umma bayan asarar rayuka da dukiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here