Gwamnatin tarayya zata hana kungiyar ASUU shiga yajin aiki

0
52

Ma’aikatar ilimi ta kasa tace tana yin kokarin hana kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU shiga wani sabon yajin aiki.

Shugabar sashin yada labarai ta ma’aikatar Folasade Biriowo, ce ta sanar da hakan ranar lahadi a birnin tarayya Abuja.

Ma’aikatar ilimin tace sun yi duk wani shirin daukar matakan hana kungiyar ASUU shiga yajin aiki, inda suka ce sun shirya wata tawagar dake aikin nemo bakin zaren magance kalubalen da ke tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya.

Karanta karin wasu labaran:ASUU ta bawa gwamnati wa’adin kwanaki 14

A makon daya gabata ne ASUU ta bawa gwamnati wa’adin kwanaki 14 akan ta biya musu bukatun su ko kuma su dauki mataki na gaba, wanda zai iya kasancewa tafiya yajin aiki.

Daga cikin bukatar kungiyar malaman jami’o’in akwai cika alkawuran yarjejeniyar da ke tsakanin ASUU da gwamnatin tarayya tun a shekarar 2009, da Kuma biyan malaman albashin watanni 8 da suka shafe a yajin aikin shekarar 2022.

Haka zalika sun bukaci gwamnatin ta biya malaman jami’o’in hakkin su na ma’aikatan dake karkashin shirin koyarwa a jami’o’i biyu, da biyan masu aikin wucin gadi, sai Kuma bukatar cire su daga tsarin biyan albashin bai daya na IPPIS.

Bayan wadannan bukatu ASUU tace dole ne gwamnatin ta saki kudaden gyaran jami’o’in da aka saka cikin kasafin kudin Nigeria na shekarar 2023.

A ranar larabar data gabata ne shugaban kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU Emmanuel Osodeke, cikin wata sanarwar daya fitar yake cewa kungiyar tana yin takaici akan sakacin da gwamnati ke yi da jami’o’i wanda yace hakan yana rage daraja da ingancin jami’o’in kasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here