Shugaba Tinubu zai yi jawabin yancin kai da safiyar Talata

0
60

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, zai yiwa yan kasa bayanin murnar bukukuwan cikar Nigeria shekaru 64 da samun yancin kai.

Shugaban kasar zai yi jawabin da misalin karfe 7 na safiyar gobe Talata 1 ga watan Oktoba.

Mai taimakawa shugaban kasar a fannin yada labarai da tsare tsare Bayo Onanuga, ne ya sanar da hakan a yau litinin.

Yace shugaban zai yi jawabin ne don nuna farin cikin zagayowar ranar da Nigeria ta samu yanci daga turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya.

A cewar Onanuga, kafafen yada labarai da suka shafi Radio da talbijin na kasa duk zasu yada jawabin na Tinubu.

Jawabin da shugaban ya yiwa yan Nigeria na karshe shine wanda aka gan shi lokacin zanga zangar neman kyakyawan shugabanci a watan Ogusta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here