Abubuwan da jawabin shugaban Nigeria na yau ya kunsa

0
43

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya gabatar da jawabin murnar cikar Nigeria shekaru 64 da samun yancin kai a safiyar yau, wanda aka haska a gidan talbijin na kasa, ta bayyanawa a kafafen Radio.

Nigeria dai ta samu yancin kai daga turawan mulkin mallakar kasar Burtaniya a ranar 1 ga watan Octoba na shekarar 1960.

A lokacin jawabin, Tinubu, yace gwamnatin sa tana yin duk mai yiwuwa don saukakawa mutane kuncin rayuwa da talauci da suke fuskanta.

Na damu matuka Kuma ina sane da irin kuncin rayuwa da tsadar rayuwa da kuke ciki, sannan mun sani mutane da yawa suna nemawa kansu hanyar da zasu samu madogarar rayuwa saboda Wannan kunci da kuke ciki, naji kukan ku Kuma zan yi maganin matsalar, a cewar shugaban.

Ya nemi yan Nigeria su cigaba da jurewa sauye sauyen da yake kawo wa masu haddasa kunci ga yan kasa, inda yace an fara ganin amfanin canjin gwamnatin sa ta kawo.

A fannin tsaro yace sun dauki matakin kawo karshen Boko Haram, garkuwa da mutane, aikin yan fashin daji, da sauran ayyukan ta’addanci.

Yace a cikin shekara daya gwamnatin sa ta hallaka manyan mayakan boko haram, da yan fashin daji masu yawan gaske.

Yace akalla manyan mayakan boko haram da sauran manyan yan ta’adda 300, jami’an tsaro suka kashe a yankin arewacin Nigeria, da sauran sassan kasar.

A bangare na kasuwanci da habbaka tattalin arziki yace sun janyo hankalin masu zuba jari daga ketare, wanda a cikin shekara guda kasashen waje suka zubawa Nigeria jarin dala biliyan 30 ko fiye da haka.

Sannan yace gwamnatin sa zata bayar  da damar yin kasuwanci babu tarnaki, da inganta dokokin da zasu taimakawa fannin kasuwanci da masana’antu ta yadda zasu yi aiki cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yace lokacin da ya hau mulki ya gaji kudaden Nigeria dake asusun ketare da yawan su yakai dala biliyan 33, sannan ya biya wani kaso daga bashin da ake bin kasar har dala biliyan 7.

Yace ya rage yawan bashin da ake bin Nigeria daga kaso 97 zuwa 68, inda yace du da haka kasar tana da asusun ketare dauke da dala biliyan 37.

Yace gwamnatin sa tana samun nasara a manufofin kudin da take kawo wa, karkashin jagorancin babban bankin kasa.

A cikin jawabin yace gwamnatin sa ta samu nasarar juya mutane daga yin amfani da makamashi mara kyau zuwa yin amfani ingantaccen makashi.

Muna yin kokarin gina wa Nigeria babban tattalin arziki, tare da bukatar samun zaman lafiya da hadin kan yan Nigeria baki daya da neman su kaunaci juna.

Yace dole Nigeria tayi gyara da sauya wasu manufofin ta ko kuma kasar ta cigaba da tafiya akan hanya mara inganci da rashin sanin makomar a gaba.

A bangare na noma kuwa ya godewa Gwamnonin jihohin Jigawa, Kebbi, da sauran su wanda yace sun dauki matakin tabbatar da manufar gwamnatin sa ta inganta fannin aikin gona da samar wa Nigeria abincin da ake bukata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here