Malam Nasir El-Rufa’i zai rantse da Al-Qur’ani akan zargin sata

0
66

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya ce bai saci kudin al’ummar jihar ba lokacin daya mulke ta.

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan a yau lokacin da ake hira dashi a tashar Radiyon Freedom Kaduna.

Yace ya mallaki duk wani abun duniya da ake ganin sa dashi tun kafin ya hau mulkin Kaduna.

Karanta karin wasu labaran:Abubuwan da jawabin shugaban Nigeria na yau ya kunsa

Majalisar dokokin jihar Kaduna tayi zargin an Sace kudin da yawan su yakai naira biliyan 423, daga farkon mulkin El-Rufa’i, zuwa karshe tsawon shekara 8.

Amman a hirar da aka yi da shi yau, ya musanta zargin.

Malam Nasir El-Rufa’i, yace lokacin karbar shugabanci shugabanni suna yin rantsuwa da Al-Qur’ani kan ba zasu ci amanar al’ummar da suke jagoranta ba.

Inda yace a yanzu ma a shirye yake yayi rantsuwa da Al-Qur’ani cewa bai saci kudin al’ummar jihar Kaduna ba.

A cewar sa yana yin addua’r Allah ya tsare shi daga cin amanar al’ummar da suka dora masa nauyi.

El-Rufa’i, yace hukumonin EFCC da ICPC, sun fara gayyatar mutanen da ya nada mukamai a gwamnatin sa don bincikar su da zargin satar kudaden al’umma, inda yace ana yin hakan don bata masa suna, sai dai yace tuni yayi addu’a akan hakan Kuma ya bar komai a wajen Allah (SWA).

KADUNA

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here