Rundunar Hisbah ta hana zancen dare tsakanin masoya a Kano

0
85
Hisbah
Hisbah

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi duba akan kukan da wasu al’ummar Kano suka kai mata game da wasu lamuran rashin tarbiyyar da ke faruwa a kwaryar birnin jihar.

Haka ne ya sa hukumar ta dauki matakan shawo kan wasu daga cikin abubuwan da ake ganin suna lalata tarbiyar yara da kuma kara munanan dabi’u a cikin al’umma.

Karanta karin wasu labaran:Hisbah ta kama matar da ke bayar da hayar dakin ta ana lalata mata

A cikin matakan da hukumar ta dauka, sun hada da haramta Zancen Dare a Mota, sannan hukumar Hisbah ta haramta zaman da samari da ‘yan mata ke yi cikin mota da dare, saboda haka ya saba wa tarbiyya da koyarwa ta Islama.

Haka zalika hukumar tace zata yi kokarin rufe Gidajen da Suke Cikin Unguwanni ana yin amfani da su don bata tarbiyar Yara.

Har ila yau an haramta yawan fita dare ga mata ba tare da wani dalili na gaskiya ba, domin kaucewa fadawa cikin hali mara kyau.

Sauran matakan sun hadar da hukunta masu daukar Mata a abubuwan Sana’ar sufuri a cikin dare don kai su wajen lalata.

Hisbah ta Kuma jaddada dokar da ta haramta bara a titunan Kano, tana kuma gargadin mabarata masu kwana a kasuwanni da tituna cewa dokar tana nan daram.

Hukumar ta ja hankalin masu otel da shagunan da ake shan giya cewa haramun ne shan giya a Jihar Kano, kuma za a dauki mataki a kansu.

Bayan wadancan matakan Hukumar Hisbah ta gargadi mata masu tsayawa a tituna da sunan tallan kansu da su tuba su bar wannan sana’a, domin ba za a lamunce da irin wannan dabi’a ba.

A cewar hukumar Hisbah, jami’anta sun bazu a lungu da sakon Jihar Kano domin tabbatar da bin dokokin da gwamnatin Kano ta kafa na yaki da lalata tarbiyyar al’umma.

Sun kuma bukaci al’umma da su rika kawo rahoton wuraren da ake gudanar da abubuwan da ba su dace ba, domin kare mutuncin jihar Kano da kuma addinin muslinci don gujewa fadawa cikin fishin Ubangiji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here