Yan ta’adda sun kashe dan takarar Kansila a Kaduna

0
62

Wasu yan ta’adda sun kashe dan takarar Kansila na jam’iyyar PDP a mazabar Pari, a karamar hukumar Kauru dake jihar Kaduna mai suna Raymond Timothy da dan uwansa James Timothy.

Barnabas Chawai, shine jagoran PDP a karamar hukumar ta Kauru, ya tabbatar da kisan mutanen a ranar lahadi lokacin da suke hanyar dawo wa daga yakin neman zabe a kauyen Kizachi, duk dai a mazabar Pari.

Karanta karin wasu labaran: An zargi sojoji da kisan fararen hula a jihar Kaduna

Yace an harbe su lokacin da suke tafiya akan babur din su mai kafa biyu, sannan yayi zargin cewa siyasa ce tasa aka kashe dan takarar Kansilan da dan uwansa.

Mamacin ya bar yara uku da mace dauke da ciki.

Jam’iyyar PDP, ta nemi jami’an tsaro su gaggauta binciko masu laifin don hukunta su da Kuma hana faruwar hakan a nan gaba, sakamakon cewa lokacin zaben kananun hukumomi a jihar yana kara kuratowa.

Ranar 19 ga watan October, shine lokacin da aka tsara don gudanar da zaben kananun hukumomin jihar Kaduna.

Sakataren dagacin garin da abin ya faru John Wanneh, shima ya tabbatar da faruwar lamarin, sannan yace kafin kisan nasu ya kasance tare da mamatan, kuma bayan mintuna 15 aka hallaka su.

Rahotanni sun tabbatar da cewa jami’an tsaro basa zuwa kauyen saboda rashin kyawun hanya, kuma akwai ruwan da se an tsallake shi kafin isa kauyen.

Zuwa lokacin rubuta Wannan labari ba’a samu damar jin ta bakin rundunar yan sandan jihar Kaduna kan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here