Akwai bukatar dauko hayar jami’an tsaro a Nigeria——NDUME

0
46

Dan majalisar dattawa mai wakiltar kudancin Borno Sanata Ali Muhammad Ndume, yace akwai bukatar shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya dauko hayar jami’an tsaro na wucin gadi don samar da tsaro, da kawo karshen mayakan boko haram a jihar Borno.

Ndume, ya yabawa kokarin da jami’an soji da yan sa kai a aikin da suke yi na samar da tsaro a jihar, inda yace jami’an basu da cikakkun kayan aikin da zasu kawo karshen mayakan boko haram.

Ndume, ya kafa hujja da cewa a kowanne yanki na duniya ana iya daukar hayar jami’an tsaro don kawar da wata matsalar rashin tsaro, kuma ya kamata ayi hakan a Nigeria.

Karanta karin wasu labaran:Yan Boko Haram sun yanka manoma a jihar Borno

Yace in an dauko hayar jami’an zasu yi aiki tare da jami’an Nigeria wajen kawo karshen mayakan boko haram da rashin zaman lafiya a yankin arewacin Nigeria baki daya.

 Bayanin nasa yazo jim kadan bayan mayakan boko haram sun kashe wasu manoma a karamar hukumar Gwoza, su biyar ta hanyar yanka su.

Awanni kadan bayan shugaban kasa Tinubu, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, sun bawa manoma tabbacin cewa gwamnati zata kare rayukan su, an samu wasu mayakan boko haram sun yiwa manoma 5 yankan rago a garin Ngoshe, dake karamar hukumar Gwoza.

Tinubu da Zulum, a jawabin da suka gabatar jiya Talata yayin bikin cika shekaru 64 da samun yancin kai da Nigeria tayi, sun ce manoma zasu samu tsaro ta yanda basu da fargabar zuwa gona don samar wa Nigeria abincin da ake bukata.

Shi kuwa Tinubu cewa yayi gwamnatin sa ta samu nasara akan Boko Haram tare da kashe manyan mayakan ta.

Masu majiyoyi sun ce manoman a baya anyi garkuwa da su, sannan aka kashe su, inda mayakan suka kashe wani dan kungiyar tsaron sa kai ta CJTF, mai suna Jubril Zarana, wanda yake aikin samar da tsaro tare da jami’an tsaro.

Wata majiya mai tushe daga Gwoza ta bayyana damuwar ta akan garkuwar da akayi da manoman su 15 wanda suka kunshi maza, mata, da kananun yara, kuma daga cikin wadannan mutane ne aka kashe biyar.

Mayakan sun yiwa manoman kwantan bauna lokacin da suka shagala da aiki a gonakin su.

Ance jami’an tsaro da yan sa kai sun yi iya bakin kokari wajen ceto mutanen da aka sace amma burin su bai cika ba, an kashe jami’in sa kai Jubril Zarana, lokacin da yake kokarin tsare rayuwar mutane.

Manoman da boko haram ta yanka bayan yin garkuwa da su sun hadar da Isa Musa Moh’d Diyara, Doglas, Salawuddin Suleman Dauda Lawan, Maryam Gwambran, Matan Kaka Mobil Aga da Baba Amos.

Bayan kashe mutane biyar sun Kuma saki mata uku, tare da rike sauran.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here