An tsinci naira miliyan 8.6 a inda wani hatsari ya faru

0
60

Jami’an hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa (FRSC), sun gano kudaden da yawan su yakai naira miliyan 8 da dubu dari 6, a wajen da wani hatsarin mota ya faru ranar litinin.

Kwamandan shiyya na (FRSC) Kabir Nadabo, ne ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a Kaduna ranar Talata.

Nadabo, yace hatsarin ya afku a unguwar G-Samaru daf da hanyar Zaria zuwa Funtua, hakan kuma yayi sanadiyyar jikkatar mutane biyu.

Yace hatsarin ya afku tsakanin motar sojojin kasar nan mai kirar Ford, da wata mota kirar Toyota Corolla.

Karanta wasu labaran:Yan ta’adda sun kashe dan takarar Kansila a Kaduna

Hukumar kiyaye afkuwar haduran, tace matukin mota Toyota wanda yake kan hanyar zuwa Zaria shine yake yin gudun wuce sa’a har hakan ya sa motar da kufce masa ya kasa tafiyar da ita.

Nadabo, ya tabbatar da cewa gudun da ake yi da ababen hawa shine musabbabin hatsarin.

Bayan kammala binciken faruwar lamarin an tabbatar da samun manyan raunuka ga mutane 3, sai mutum daya da bai ji ciwo ko kadan ba.

Tuni aka mika wadanda suka jikkata zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, dake shika

Adadin kudin da aka samu a wajen hatsarin naira miliyan 8 da dubu dari 6 sun kasance mallakin mai mota kirar Toyota Corolla, Kuma za’a mika masa kudin da zarar ya kammala farfadowa daga yanayin da yake ciki na jin ciwuka saboda hatsarin, kamar yadda Nadabo ya tabbatar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here