Masu Zuwa Mauludin jihar Niger su 150 sun nutse a ruwa 

0
86

Akalla mahalarta taron maulidi 150 ne suka nutse tafkin Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa, a jihar Niger.

Jirgin ruwan da mutanen ke ciki yana dauke da mutane 300.

Daily Trust, ta rawaito cewa mafi yawancin wadanda suka fuskanci nutsewar mata ne da kananun yara, wanda suka fito daga garin Mundi a jiya Talata.

Karanta karin wasu labaran:An kuɓutar da mutum 120 da ke cikin jirgin ruwan da ya kama da wuta

Wani mazaunin garin daya zanta da manema labarai, yace masu Sana’ar tuka jiragen kwale-kwale sun yi kokarin ceto mutanen da aka samu suna da rai.

Hatsarin ya afku da misalin karfe 8:30 na dare jim kadan bayan mahalarta taron sun shiga jirgin ruwan.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Niger Alhaji Abdullahi Baba Arah, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai bayyana adadin yawan mutanen da suka mutu ba.

Yace sun samu rahoton nutsewar mutane mahalarta taron maulidi a cikin ruwa yawancin su mata da kananun yara wanda suka fito daga garin Gbajibo dake karamar hukumar Mokwa.

Tuni dai gwamnatin jihar ta bayar da umarnin gaggauta kai dauki ga wadanda iftila’in ya afkawa tare da binciko wadanda ba’a gani ba, sannan mutanen gari suma sun bayar da tasu gudunmawar ceton.

Yace tuni aka tseratar da mutane 150, da ran su, Kuma a halin yanzu ana cigaba da binciko wadanda ba’a gani ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here