Matasa sun yi zanga zanga akan cire shugabar hukumar zabe

0
77

Jerin gwanon wasu matasa sun gudanar da zanga zangar neman a gaggauta cire shugabar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC reshen jahar Ondo, Oluwatoyin Babalola, daga mukamin ta.

Matasan sun mamaye babban ofishin hukumar INEC na jihar dake Akure, bisa zargin ta hada kai da wasu yan siyasar jihar gabanin gudanar da zaben gwamnan Ondo dake tafe.

Karanta karin wasu labaran:A karon farko an gudanar da zaben kananun hukumomi a Anambra

INEC, ta saka ranar 16 ga watan Nuwamba mai kamawa a matsayin ranar gudanar da zaben gwamnan, wanda jam’iyyun siyasa 17 zasu shiga.

Fusatattun matasan dauke da kwalaye masu mabanbantan rubutun nuna kin jinin kwamishinar zaben sun ce cigaba da kasancewar Babalola, a mukamin babbar barazana ce ga zaben gwamnan jihar ta Ondo.

Daya daga cikin masu zanga zangar da yayi magana da manema labarai a madadin daukacin mutanen dake yin boren mai suna Olawale, ya ce suna zargin Babalola, da hada kai da wasu yan jam’iyyar APC jihar.

Olawale, ya Kuma yi zargin cewa shugabar hukumar zaben tana dauke da katin shaidar zama yar jam’iyyar APC, sannan dole ta ajiye mukamin ta kafin a shiga zabe.

Sun roki shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC Farfesa Mahmud Yakubu, ya nada sabon shugaban hukumar zaben jihar, sannan a saka musu wanda bashi da bangarancin siyasa.

Duk yunkurin da akayi don jin ta bakin kwamishinar haka bai samu ba, sakamakon ta kashe wayar hannun ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here