NNPCL ya bawa Matatar Dangote gangar mai miliyan 48

0
91

Kamfanin mai na NNPCL, yayi safarar gangar danyen man fetur miliyan 48 da dubu dari 6, zuwa ga matatar man fetur ta Dangote a watanni 10 da suka wuce.

Wani binciken jaridar Vanguard, ne ya gano bayanan safarar danyen man.

Binciken ya nuna cewa an bawa Matatar Dangote gangar mai miliyan 3 da dubu dari 4, a watan Disamba na shekarar 2023, sai a watan Fabrairun shekarar da muke ciki an basu ganga miliyan 3 da rabi.

Karanta karin wasu labaran:Dillalan man fetur sun daina siyan mai daga matatar Dangote

Haka zalika wata majiyar daga matatar man fetur ta Dangote, tace adadin yayi mata kadan idan aka yi la’akari da cewa zasu iya tace gangar danyen man dubu 650 a kowacce rana.

Kawo yanzu dai kamfanin NNPCL bai bayyana adadin danyen man fetur da matatun man fetur na kasar nan zasu bukata ba a watanni 3 na karshen shekarar 2024.

A baya al’ummar Nigeria sun yi zaton samun saukin farashin man fetur da zarar matatar man fetur ta Dangote ta fara tace man, sai dai hakan ya gagara, lokacin da aka samu karin farashin man bayan fara fitar da tataccen man da Dangote yayi zuwa kasuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here