Babbar kotun tarayya dake birnin tarayya Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, akan naira miliyan 150, a shari’a da hukumar EFCC ta gurfanar da shi kan zargin wawure dukiyar jihar da takai naira biliyan 27 lokacin mulkin sa.
Mai shari’a Sylvanus Chinedu Oriji, ne ya bayar da belin kuma ya nemi Ishaku ya kawo mutane biyu da zasu tsaya masa.
Karanta karin wasu labaran:EFCC ta kama tsohon gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku
An gurfanar da Ishaku, tare da tsohon babban sakataren hukumar kula da kananun hukumomin Taraba Bello Yero, kan zargin su da aikata lefuka15, na cin amanar al’ummar da suka shugabanta ta hanyar zargin sace adadin wadancan kudade na kananun hukumomin Taraba.
Mutanen da zasu tsaya har a bayar da belin Ishaku dole ne su kasance suna da matsayin aiki na darakta a matakin gwamnatin tarayya, kuma dole ne mutanen su kasance mazauna birnin tarayya Abuja.
Sannan an haramtawa Ishaku da Yero, fita daga Nigeria ba tare da sani ko izinin kotu ba.
Lauyoyin dake kare wadanda ake kara ne suka roki kotu ta bayar da belin, wanda lauyan dake kare hukumar EFCC da ta shigar da karar bai kalubalanci bayar da belin ba.
Mai shari’a Oriji, ya jingine sauraron karar har zuwa ranakun 4, 5, da 13, na wata mai kamawa wato Nuwamba.