Bello Turji ya ce zai mikawa gwamnati makaman sa

0
81

Fitaccen Dan fashin dajin nan Bello Turji, ya kalubalanci jami’an tsaro tare da ikirarin cewa ko kadan baya tsoron mutuwa

Sai dai kuma ya bayar da kofar tattaunawa da gwamnatin tarayya akan kawo karshen ayyukan ta’addanci a jihar Zamfara.

Turji, wanda yake daya daga cikin manyan yan fashin dajin da suka addabi arewacin Nigeria su 48, kuma shalkwatar tsaro ta ayyana su a matsayin wadanda take nema ido rufe, yayi Wannan jawabi a wani faifan bidiyo na tsawon mintina 5.

Karanta karin wasu labaran:Gwamnatin Zamfara tayi alkawarin chanzawa mutanen da ambaliyar ruwa ya shafa

Turji, a faifan bidiyon ya tabbatar da kisan da aka yiwa mai gidan sa Halilu Sububu, tare da cewa kashe mai gidan nasa ba zai hana shi aiwatar da aniyar sa ta ta’addanci ba.

Turji, ya kara tabbatar da cewa a shirye yake ya zubar da makaman sa zuwa ga gwamnati in har gwamnatin zata saurari bukatun sa.

Amman yace a kowanne lokaci a yana zaune da shirin ko ta kwana akan mutuwa.

Haka zalika yace sai an dena kashe yan uwan su, sannan zasu kyale al’ummar Zamfara su zauna lafiya.

A wani bangaren Turji, yace gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan, da ministan tsaro Bello Matawalle, ba zasu taimakawa al’ummar Zamfara ba wajen samar da tsaro, inda yace yan siyasa ne da basu da niyyar taimakon al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here