Gwamnoni sun fara shirin hana bawa kananun hukumomi kudi kai tsaye

0
33

Gabanin aiwatar da rahoton kwamitin mutane 10 da aka kafa akan aiwatar da fara bawa kananun hukumomi kudin shigar su kai tsaye daga gwamnatin tarayya, wanda kotun koli ta zartar da hukunci akan hakan, Gwamnonin kasar nan sun fara rokon gwamnatin tarayya ta dakatar da fara bawa kananun hukumomin kudin su kai tsaye.

Kananun hukumomi dai suna karbar kason da gwamnatin tarayya ke basu ta hannun asusun gwamnatocin jihohi.

Karanta karin wasu labaran:Kotu ta hana jam’iyyu 19 kawo wa KANSIEC matsala a zaben kananun hukumomin Kano

Kwamitin da aka kafa karkashin sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya kammala aikin sa, Kuma ana zaton kwamitin zai mika rahoton sa a ranar 13, ga watan da muke ciki.

Tun a gwamnatin tsohon shugaban kasa Buhari, aka yi kokarin, dakatar da turawa kananun hukumomi harajin da ake tattarawa ta cikin asusun gwamnatin tarayya, da Kuma haramtawa kananun hukumomi fitar da kudin da yawan su ya zarce naira dubu dari 5 a kowacce rana.

Sai dai a wancan lokaci Gwamnonin kasar nan nan karkashin kungiyar su ta NGF, sun yi fatali da Wannan yunkuri da Buhari ya dauki niyyar aiwatar wa.

A watan Mayun shekarar da muke ciki ne gwamnatin tarayya ta shigar da kara gaban kotu tana kalubalantar gwamnatocin jihohi akan dena turawa kananun hukumomi kudin su ta karkashin asusun gwamnatin jiha, saboda ana zargin jihohin da rike kason kananun hukumomi.

A cikin karar da gwamnatin ta shigar ta kuma nemi a haramtawa jihohi cire zababbun shugabannin kananun hukumomi daga mukamin su har sai sun kammala wa’adin mulkin su da kuma haramtawa jihohi nada shugabannin rikon kwarya.

Hakan ne yasa kotun koli zartar da hukunci a ranar 11 ga watan Yulin shekarar da muke ciki, cewa babu gwamnatin jihar da take da hurumin yin yanda take so da kudin karamar hukuma.

NGF

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here