Kotu zata yanke hukuncin hana Sarkin Kano na 15 gyara gidan Nassarawa

0
72

Babbar mai shari’a ta jihar Kano, Dije Aboki, ta tsayar da ranar 10 ga watan October a matsayin ranar yanke hukunci akan karar da aka shigar ta neman hana Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, yiwa gidan sarki na Nassarawa kwaskwarima.

Gidan Nassarawa shine wajen da Sarkin na 15 yake zaune tun bayan lokacin da gwamnatin Kano ta sauke shi daga sarautar Kano.

Karanta karin wasu labaran:Yan sanda sun kama masu shirya zanga zanga a jihar Kano

Gwamnatin jihar Kano ce ta shigar da karar neman hana Sarkin aiwatar da aniyar sa ta gyara gidan na Nassarawa, ta hannun lauyan ta Rilwanu Umar mai lambar kwarewa ta SAN, a ranar 12 ga watan Satumba.

A kwanakin baya ne aka jiyo bangaren Alhaji Aminu Ado Bayero, na shirin yin wasu gyare-gyare a mazaunin nasa, duk da cewa gwamnatin Kano bata amincewa zaman da yake yi a gidan ba, bayan sauke shi daga sarautar Kano.

Haka ne yasa gwamnatin daukar matakan rushewa tare da gyara wasu bangarorin gidan Nassarawa, har ma ta bayyana adadin kudaden da za’a kashewa aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here