Za’a dakatar da ababen hawa a Jigawa saboda zaben kananun hukumomi

0
53

Rundunar yan sandan jihar Jigawa ta sanya dokar takaita zirga zirgar ababen hawa a fadin jihar daga karfe 12 na daren juma’a zuwa 6 na yammacin asabar, saboda shirin gudanar da zaben kananun hukumomi.

Rundunar tace a tsakanin Wannan lokaci ba za’a bar mutane suyi zirga zirga da ababen hawa ba, sai dai masu ayyuka na musamman.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP Lawan Shisu Adam, ne ya sanar da hakan a yau Alhamis.

Karanta karin wasu labaran:Matsin rayuwa: Magidanci ya rataye kansa har lahira a Jigawa

Yace wadanda aka amince su yi yawo da ababen hawa a ranar asabar sun hadar da motar dauko marasa lafiya, masu saka idanu akan zaben, da masu kashe gobara.

Ya kara tunatar da jam’iyyun siyasa cewa haramun ne yin bangar siyasa ayyukan daba, da yin amfani da makami a Jigawa kuma duk wanda aka samu yana yin daya daga cikin wadannan laifuka a lokacin zaben zai fuskanci hukunci.

Sannan ya shawarci duk masu son tayar da hankalin al’umma su canja tunani da Kuma neman suyi biyayya ga dokokin zabe.

Rundunar yan sandan ta kara da cewa babu wani jami’in tsaro da aka amince ya yi rakiya ga mai gidan sa zuwa rumfar zabe.

Har ila yau, rundunar yan sandan jihar ta Jigawa tace zata yi aiki da sauran jami’an tsaro wajen dakile duk wani yunkurin tayar da zaune tsaye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here