Gwamnan jihar Rivers Fubara, ya zargi shugaban yan sanda na kasa Kayode Egbetokun, da nuna bangaranci a yanayin tafiyar da aikin sa, sannan gwamnan yace babu wanda zai hana gudanar da zaben kananun hukumomin jihar.
Fubara, sanar da hakan a daren jiya lokacin da yakai ziyara babban ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar RSIEC, sannan ya samu rahoton cewa akwai hannun yan sandan a matsalolin da gudanar da zaben kananun hukumomin jihar ke fuskanta a yanzu.
Yace a cikin hukuncin da kotun tarayya ta yanke akan zaben jihar, babu wajen da aka haramta gudanar da zaben.
karanta karin wasu labaran:Yan sanda sun janye hannun su daga zaben jihar Rivers
Idan za’a iya tunawa rundunar yan sandan jihar Rivers tace zata yi cikakkiyar biyayya ga umarnin wata babbar kotun tarayya wadda ta yanke hukuncin hana rundunar yan sandan bayar da tsoro a lokacin gudanar da zaben kananun hukumomi a jihar ta Rivers.
Jawabin yan sandan yazo bayan awanni 24 da magoya bayan jam’iyyar PDP suka gudanar da zanga zangar kin jinin gudanar da zaben.
Masu zanga zangar da suka hadar da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Rivers, sun halarci ofishin hukumar zaben jihar da shalkwatar yan sandan jihar harma da ofishin hukumar tsaron farin kaya DSS, don suyi biyayya ga umarnin hana jami’an tsaro zuwa wajen zaben.
Amman yan sandan sun ce hakan baya nufin zasu saka idanu ana aiwatar da tashin hankali ba tare da daukar mataki ba, tare da cewa zasu yi aikin su na kiyaye afkuwar tashin hankali a tsakanin al’umma.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Rivers Grace Iringe-Koko, ce ta bayyana hakan a Fatakwal ranar Alhamis.
Masana harkokin siyasa na alakanta Wannan kalubalen da gwamnan jihar Rivers ke fuskanta akan rikicin dake faruwa tsakanin sa da ministan birnin tarayya Abuja Nyesom Wike.